Olivier Giroud ya koma Arsenal

Olivier Giroud Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Olivier Giroud

Arsenal ta kammala yarjejeniyar sanya hannu a kwantiraginta da Olivier Giroud daga Montpellier a kan fam miliyan 12.

Dan wasan mai shekaru 25 dan kasar Faransa ya kammala jarrabawar duba lafiyarsa da kuma dukkanin wasu rubuce rubuce tsakaninsa da kungiyar ta Arsenal ranar litinin.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya dauko dan wasan ne da nufin amfani da shi a gaba inda zai hada shi da wani sabon dan wasn Lukas Podolski da Robin Van Persie.

Shi dai Giroud wanda ke bugawa Montpeller wasa sau daya ya taba bugawa kungiyar kwallon kasar a watan Nuwamba na 2011 yana da shekara 25.

Akan daukan na sa Arsene Wenger ya ce ya na farin cikin dawowa Arsenal da dan wasn ya yi wanda zai kara mu su karfi a gaba a kakar wasanni mai zuwa.

Giroud ya ciwa Montpeller kwallaye 21 kuma sau hudu a sako shi canji a wasnnin Faransa na gasar cin kofin kasashen Turai da ake yi .