An bayyana matan da za su yiwa Birtaniya wasa

kelly smith
Image caption kelly smith

An bayyan sunayen tawagar 'yan wasn kwallon kafa mata da za su bugawa Birtaniya gasar Olympics ta London 2012, da suka hada da kelly Smith bayan da ta warke daga raunin da ta yi.

Smith wadda ta ke kan gaba a Birtaniya wajen cin kwallaye ta sami sauki ne bayan da ta yi rauni a watan Maris.

Daga cikin 'yan wasan su 18 biyu ne kawai ba 'yan Ingila ba Ifeoma Dieke da Kim Little wadanda 'yan Scotlanda ne. Gasar wasannin Olympics ta London ita ce gasa ta farko ta olympics da 'yan wasan kwallon kafa matan na Birtaniya za su fara bugawa