Bolton Wanderers za ta dauki Keith Andrews

keith andrews Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption keith andrews

Ana ganin kungiyar kwallon kafa ta Bolton Wanderers za ta yi nasarar daukan Keith Andrews dan Jamhuriyar Ireland.

Dan wasan tsakiyar ya buga dukkanin wasan da Ireland ta yi a gasar wasan cin kofin kasashen Turai,Euro 2012,kuma a wasansu na karshe da kasar Italia a ka koreshi daga wasan.

Tsohon dan wasan na Blackburn da MK Dons da kuma Hull City ya ci kwallaye tara a wasanni ashirin da ya buga wa kungiyar Ipswich da a ka bata shi aro a shekarar da ta wuce.