David Beckam ba zai je Olympics ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Beckham

david beckhamTsohon kyaftin din Ingila David Beckam ba zai sami damar bugawa 'yan wasan Burtaniya na gasar Olympics da za a yi a Landan ba.

Bayan tankade da rairaya da kocin 'yan wasan Stuart Pearce, ya yi na 'yan wasa 35 wadanda a da Beckam din yana cikinsu a matsayin daya daga cikin manyan 'yan wasa uku da suka wuce shekara 23 da ake sirka matasan 'yan wasan da su, sai kocin ya zabi 18 daga ciki, ya ajiye sauran da suka hada da Beckam.

Beckam dan shekara 37 wanda yai fatan ya jagoranci 'yan wasan Olympics din na Burtaniya a matsayin kyaftin, bai ji dadin matakin ajiye shi din ba, ya ce ''banji dadi ba matuka amma duk da haka ba bu wani mai goyon bayan kungiyar da yafi ni, da an sa ni cikin wannan kungiya ta daban to da ba karamar karramawa ba ce a gare ni,kamar kowa zan yi fatan inga sun yi nasarar cin lambar gwal a gasar''.

Kafin ya sanar da matakin nasa na cire Beckam daga jerin 'yan wasan olympics din na Burtaniya kocin ya yiwa Beckam waya inda ya ce ma sa ya na son bada muhimmanci ne wajen hada 'yan wasan baya,kamar yadda jaridar the Times ta ruwaito.

Kuma kocin ya kalli wasan Beckam a kungiyarsa ta LA Galaxy a Amurka a makon da ya wuce.

Manyan 'yan wasan uku da Pearce ya zaba su ne dan wasan baya na Manchester City Micah Richards da Ryan Giggs na Manchester United da kuma dan wasan gaba na Liverpool Craig Bellamy.

Kocin ya ce nawin da ya rataya a wuyansa na Burtaniya shi ne ya hada 'yan wasan da zasu takawa kasar rawar gani a gasar, su ciyo ma ta gwal, a don haka zai yi duk abin da zai iya ya hada kungiya mai karfi.

A wasan kwallon kafar na Olympics na Landan an sanya kungiyar Burtaniyan ce a rukuni na daya, Group A, da ya kunshi Senegal da Uruguay da Amurka da kuma Hadaddiyar Daular larabawa.