Fafatawar Jamus da Italiya in an jima

Tambarin Jamus da Italiya
Image caption Tambarin Jamus da Italiya

Idan an jima ne da karfe 7:45 na dare agogon Najeriya, za a kara tsakanin kasar Jamus da Italiya a wasan kusa da na karshe kashi na biyu na gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Turai, Euro 2012 a babban filin wasa na Warsaw.

Duk da cewa Bastian Schweinsteiger ya yi jiyyar wani rauni da ya ji a agararsa, kocin Jamus Joachim Loew ya ce dan wasan ya sami sauki sosai a don haka zai buga wasan.

Kuma ana ganin kocin zai yi amfani da sauran gwanayen 'yan wasansa da ya ajiye a wasansu da Girka, wadanda suka hada da Mario Gomez da Lukas podolski da kuma Thomas Mueller.

A nasa bangaren kocin Italiya Cesare Prandeli,na fuskantar matsalar rashin tabbas akan lafiyar wasu 'yan wasansa,irin su Giorgio Chiellini da Daniele De Rossi da kuma Ignazio Abate, wanda ake ganin zai sake amfani da tsarin barin 'yan wasa uku a baya in har ta tabbata Abate ba zai iya yin wasan ba ,tun da an dakatar da Christian Maggio.

Game da halin lafiyar 'yan wasan na Italiya likitan kungiyar Enrico Castellaci ya ki ya bada tabbacin halin da suke ciki ko za su iya buga wasan na yau Alhamis ko ba za su iya ba, illa dai yana baiwa magoya bayansu tabbacin cewa su na yin iya kokarinsu akan 'yan wasan.

Wasan dai ana ganin abubuwa biyu ne suka mamaye shi, abubuwan sune , tsoro da kuma ramuwa.

Rashin isasshen hutun da 'yan wasan Italiya suka fuskanta bayan wasansu na baya , inda suka huta na kwanaki biyu kawai da kuma irin yadda wasan ya kaisu zuwa karin lokaci,sai dai abin da ya ke basu kwarin guiwa shi ne cewa a duk karawar da suka taba yi da Jamus sau bakwai a baya , Jamus ba ta taba samun nasara akansu ba. Dan wasan da yai fice a gasar zuwa yanzu, Andrea Pirlo dan Italiya yace '' tsoron mu suke-mun kai matsayin Spain''.

Karin bayani