Spain ta fidda Portugal a Euro 2012

'yan wasan spain Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'yan wasan spain

Bayan da aka fafata tsakanin Spain da Portugal tsawon mintina casa'in da kuma karin mintina talatin ba wadda ta sami nasarar jefa kwallo tsakanin kasashen biyu a wasan kusa da na karshe, Spain ta sami galaba akan Portugal a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci 4 da 2.

Dukkanin kasashen biyu sun kasa cin bugun fanaretinsu na farko, inda maitsaron gidan Portugal Rui Patricio ya fara ture bugun Xavi Alonso, sai shima Casillas na Spain ya kade bugun Muotinho.

Andres Iniesta shi ne ya fara ciwa Spain sannan Pepe ya ramawa Portugal, daga nan kuma sai dan wasan bayan Spain Gerard Pique ya sami sa'ar cin bugunsa,amma Nani ya maida wasan 2 da 2.

Daga nan ne kuma sai Sergio Ramos ya jefawa Spain kwallonta ta uku,amma Daniel Alves ya barar wa Portugal bugunsa,wasa ya zama Spain na da ci 3 Portugal kuma na da 2.

Fabregas shi ne ya kawo karshen wasan bayan da ya ci kwallo ta 4,abin da ya baiwa Spain nasara da ci 4 da 2, da hakan ta basu damar zuwa wasa na karshe tsakaninsu da kasar da za ta sami nasara tsakanin Italiya da Jamus a wasan da za suyi ranar Alhamis din nan.