Yohan Blake ya sake tserewa Usain Bolt

bolt da blake Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bolt da Blake

Yohan Blake ya wuce Usain Bolt wanda ke da lambar zinariya uku ta wasan Olympics,a tseren mita 200 na gwaji tsakanin wadanda zasu wakilci Jamaica a wasan Olympics da za a yi a London.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin kwanaki uku da zakaran wasan tseren na duniya Usain Bolt ya ke shan kashi a hannun takwaran nasa dan jamaica, inda a ranar Juma'a ma Blake din ya wuce shi a gudun mita 100.

Bolt wanda shi ne ke rike da lambobin zinariya na Olympics da aka yi a Beijin ta China, a tseren mita 100 da miya 200 da kuma gudun karba karba na 4x100, ya ce shi ne zakaran wasan Olympics , dole ne ya natsu ya duba abin da ya sa ya sami wannan koma baya, kuma ya shawokan matsalar.

Ya ce dole ne ya gano matsalar da ta sa shi hakan domin ya nunawa duniya har yanzu shi ne zakaran duniya, kuma sati uku ya ishe shi ya farfado.

Karin bayani