Iniesta shi ne zakaran gasar Euro 2012

andres iniest Hakkin mallakar hoto d
Image caption Andres Iniest

Hukumar kwallon kafa ta Turai ,UEFA ta bayyana dan wasan tsakiya na Spain Andres Iniesta a zaman zakaran gasar Euro 2012 da aka kammala, wadda Spain din ta dauki kofi, bayan da ta cinye Italiya 4-0.

'Yan kwamitin kwararru na hukumar ta Uefa, su ne su ka zabi dan wasan na kungiyar Barcelona,mai shekara 28, bayan da ya taka rawar gani wajen taimakawa kasarsa Spain ta dauki kofin kasashen Turan a karo na biyu a jere.

Haka kuma akwai 'yan wasan Spain din su goma da aka zaba a cikin 'yan wasa 23 da hukumar ta ce sune zakaru a gasar wadanda su ka hada da Steven Gerrard na Ingila.

Iniesta wanda ya ci wa Spain kwallonta daya da ta sanya a ragar Holland a wasan karshe na cin Kofin Duniya na 2010, ya bugawa Spain dukkanin wasanninta na gasar ta Euro 2012.

Iniesta ya kasance mai baiwa kungiyar kasar Spain kwarin guiwa kamar yadda ya ke baiwa kungiyarsa ta Barcelona a wasanninsu, inda ya taimakawa Barcelonan ta dauki kofin zakarun Turai har sau biyu ta kuma dauki kofin gasar La Liga sau uku a shekaru hudu da suka wuce.

Dan wasan tsakiya na Liverpool Gerrard da dan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic su kadai ne 'yan wasan da aka sanya a jerin zakarun 'yan wasan gasar ta Euro 2012, wadanda kasashensu ba su kai ga wasan kusa da na karshe ba.

Sauran 'yan wasan da za a karrama saboda kwazonsu a gasar a Poland da Ukraine sun hada da Andrea Pirlo na Italiya da Cristiano Ronaldo na Portugal.