Spain ce babbar kungiya a wannan zamani -Del Bosque

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Spain na murna

Kocin Spain, Vicente del Bosque, ya yaba wa ‘yan kungiyar bisa lashe kofin kwallon kafa na kasashen Turai, Euro 2012, inda ya bayyana kungiyar da cewa ita ce ‘‘babbar kungiyar kwallon kafa ta wannan zamani’’.

Ita dai kungiyar ta Spain ta lallasa Italiya da ci hudu ba ko daya a wasan karshe da suka buga a birnin Kiev na Ukraine.

Kwallo ta hudu da La Roja ya zura ita ce ta sanya kungiyar ta kasance kungiya ta farko da ta lashe gasar sau uku a jere a gasar Euro.

Del Bosque ya ce:‘‘Wannan kungiya ita ce babbar kungiya a wannan zamani.'Yan wasan sun san yadda ake buga wasa cikin tsari saboda sun fito ne daga kasar da ake yin wasa cikin nutsuwa. Wannan shi ne zamani mai karko ga ‘yan kwallon kafa na Sapin’’.

Del Bosque, mai shekaru 61 a duniya, ya kara da cewa: ‘‘Muna da wasu daga cikin ‘yan wasan da suka yi fice wajen bugawa kungiyoyin kasashen waje, wanda a baya ba haka lamarin yake ba.Ba ma bukatar ‘yan wasa daga kasashen duniya amma su suna bukatar ‘yan wasanmu’’.

Ya ce lashe gasa sau uku a jere ba karamin aiki ba ne, yana mai jinjina wa ‘yan wasan bisa kwazon da suka yi.

Karin bayani