Samir da Hatem za su fuskanci hukunci

Shugaban kasar Faransa, Francios Hollande Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar Faransa, Francios Hollande

'Yan wasan kwallon kafa na Faransa hudu za su fuskanci hukunci a kan rashin da'ar da suka nuna a gasar wasan cin kofin kasashen Turai, Euro 2012.

'Yan wasan su ne Samir Nasri wanda ya ci mutuncin wani dan jarida da Jeremy Menez wanda shi ma ya yi cacar baki da kyaftin din su Hugo Lloris sai Hatem Ben Arfa wanda ya yi musayar kalamai da kocinsu Laurent Blanc.

Sannan akwai Yann M'Vila wanda ya ki gaisawa da kocin lokacin da aka sauya shi da Olivier Giroud a wasansu da Spain ranar 23 ga watan Yuni.

Kocin Faransa da ya bar aiki bayan kwantiraginsa ya kare, Raymond domenech shi ma ya yi fama da matsalar rashin jituwa a tsakanin 'yan wasa.

Abin da ya ce ya haifar mu su da matsala kafin wasansu na gab da na kusa da na karshe da Spain wanda Spain ta fitar da su.