An sallami kocin Watford

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sean Dyche

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta sallami kocinta, Sean Dyche, kuma hakan zai ba Gianfranco Zola damar zama sabon kocin.

BBC ta fahimci cewa an shaidawa Dyche batun sallamar ta sa ne ranar Litinin.

Dyche, wanda ke da shekaru 41 a duniya, ya jagoranci kulab din daga watan Yunin shekarar 2011, kuma a kakar gasar Championshinp da ta gabata kulab din ya zo na 11 a jerin kulab-kulab da suka shiga gasar.

Iyalan Pozzo, wadanda sune suka mallaki kungiyar ta Watford sun ce tuni suka tattauna da Zola domin zama sabon kocin kungiyar.

A baya dai Dyche, dan kasar Italiya, ya jagoranci West Ham na tsawon shekaru biyu, sai dai sun babe da kungiyar a watan Mayun 2010.

Karin bayani