Villas-Boas ya zama sabon kocin Tottenham

andre villas-boas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Andre Villas-Boas

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki tsohon kocin Chelsea, Andre Villas-Boas a matsayin sabon kocinta, sati uku bayan ta kori Harry Redknapp.

Shi dai Villas-Boas ya dawo fagen harkar kwallon kafa ne a kwantiragin shekaru uku, watanni hudu bayan da Chelsea ta sallame shi daga aiki, yace wannan dama da ya samu ita ce mafi ban sha'awa a aikinsa na horad da 'yan wasa a gasar Premier.

Ya ce wannan kungiya ce da ta hada 'yan wasan da duk wani kociya zai so ya yi aiki da su, ya ce ya yi imani cewa gaba dayansu za su kai kungiyar ga nasara a kakannin wasanni da ke gaba.

Duk da nasarar da ya samu ta daukan kofin lig da na kalubale na Portugal da kuma nasara a gasar Europa a kungiyar Porto a kakar wasannin 2010 zuwa 2011,Chelsea ta kore shi daga aiki kasa da watanni goma sha biyu da fara kwantiraginsa na shekara uku da kungiyar.

Karin bayani