Robin Van Persie zai bar Arsenal

robin van persie Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Robin van Persie

Dan wasan gaba na Arsenal Robin van Persie ya bayyana cewa ba zai sabunta kwantiraginsa da kungiyar ba.

Dan wasan mai shekaru 28 dan kasar Holland, wanda ya ke da sauran shekara daya a kwantiraginsa ya tabbatar cewa ya gana da kocin klub din Arsene Wenger da kuma shugaban Arsenal din Ivan Gazidis.

Sai dai ya ce a yayin ganawar sun sami bambamcin ra'ayi da fahimta akan yadda za a ciyar da kungiyar gaba.

Van Persie ya ce ya yi dogon tunani matuka akan shawarar barin kungiyar ta Arsenal, amma a karshe ya ga ya dace ka da ya sabunta kwantiragin nasa.

Karin bayani