Kungiyar Arsenal ta fasa zuwa Najeriya

arsenal
Image caption 'Yan wasan Arsenal

Kungiyar Arsenal ta dage ziyarar da ta shirya kaiwa Najeriya domin wasan sada zumunta da tawagar 'yan wasan kasar wato Super Eagles ranar 5 ga watan Agusta.

Kungiyar ta yanke shawarar dage rangadin ne saboda abin da ta kira sarkakiyar da ke tattare da shirin zuwan nata, amma ba ta bayar da bayani dalla-dalla game da sarkakiyar ba.

Daraktan harkokin kasuwanci na Arsenal din Angus Kinnear ya ce, ''Kawo babbar kungiya kasuwar duniya abu ne da a koda yaushe ya ke da sarkakiya da kuma kalubale".

Daraktan ya kuma ce Arsenal tana da magoya baya masu yawa a Afirka, kuma suna matukar bakin ciki cewa kungiyar ba za ta yi ziyarar da aka shirya ba a wannan bazara, amma duk da haka ya ce suna da dogon buri na kyakkyawar alaka da Najeriya, kuma tuni suna shirya yadda za su kai ziyarar a badi.

Haka kuma Mista Kinnear ya ce suna da wadansu ayyuka masu kayatarwa da suka shirya gudanarwa da abokan huldarsu a Najeriya, irin su Emirates da Malta Guiness da Airtel wadanda za su fara gudanarwa a makwannin da ke tafe.

Karin bayani