Radwanska da Williams za su yi wasan karshe

agnieszka radwaska Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Agnieszka Radwaska

Za ayi wasan karshe na gasar tennis ta Wimbledon ta mata tsakanin Agneszka Radwanska da Serena Williams.

Tun da farko Agnieszka Radwanska 'yar kasar Poland ta uku a duniya a wasan ta sami nasarar zuwa babban wasan karshe na tennis a karon farko inda ta fitar da Angelique Kerber 'yar kasar Jamus a gasar Wimbledon da ake yi a Ingila.

Cikin sa'a daya kacal Radwanska, wadda ita ce 'yar Polanda ta farko da ta taba samun nasarar zuwa wasan kusa da na karshe na wani babban wasan tennis ta yi waje da Kerber.

Ta samu nasarar ce da ci 6-3 6-4, wanda sakamakon ya nuna ta sami galaba akan abokiyar karawar tata cikin sauki.

Ita kuma Serena Williams ta sami damar zuwa wasan na karshe ne bayan da ta fitar da Victoria Azarenka da ci 6-3 7-6 (8-6) a cikin sa'a daya da mintina 36.

Karin bayani