Federer ya zama zakaran Wimbledon

roger federer Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roger Federer

Roger Federer ya zama zakaran gasar tennis ta maza ta Wimbledon bayan da ya buge Andy Murray na Burtania da ci 4-6 7-5 6-3 6-4.

Wannan nasara da ya samu ta bashi damar daukan kofin Wimledon din a karo na bakwai kamar yadda Pete Sampras ya kafa tarihi kuma wannan shi ne karo na goma sha bakwai da ya ke cin kofin wata babbar gasa.

Abokin karawar tasa Andy Murray wanda wannan shi ne karon farko da ya sami zuwa wasan karshe na Wimbledon sau hudu ke nan ya na rashin nasara a karawar karshe ta manyan wasannin tennis jeri hudu na farko da ya taba zuwa, kamar kocinsa Ivan Lendl.

Kafin wannan karawa ta karshe a ranar Juma'a ce zakaran gasar na yanzu Roger Federer ya doke na daya a duniya a fagen wasan na tennis kuma mai rike da kofin gasar ta Wimbledon Novak Djokovic.

An dakatar da wasan na tsawon mintina 35 saboda ruwan sama kafin daga bisani aka cigaba.

Karin bayani