Mancini ya sabunta kwantiraginsa da City

roberto mancini Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City ya sabunta kwantiraginsa da zakarun gasar Premier na tsawon shekaru biyar.

Tun a watan Disamba na 2009 ne Roberto Mancini ya maye gurbin Mark Hughes a matsayin kocin kungiyar inda ya kai su ga samun nasarar daukan Kofin Kalubale a 2011.

Shekara daya bayan wannan kuma wato a wannan shekara ta 2012 kuma kocin ya kai kungiyar ga samun nasarar daukan Kofin gasar Premier tun shekara ta 1968.

Mancini ya shedawa shafin sadarwa na intanet na kungiyar ta Manchester City cewa ya na farin cikin ya taimakawa kungiyar ta yadda duk zai iya na karin wasu shekaru biyar, ya kara da cewa damar dorawa akan nasarar da muka samu ta baya bayan nan ta na da yawa.

Karin bayani