Park Ji-sung ya koma QPR daga United

park_ji_sung Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Park Ji-sung

Queens Park Rangers sun kammala yarjejeniyar daukan Park Ji-sung daga Manchester United.

Rangers za ta fara biyan fam miliyan biyu a kan dan wasan mai shekara 31,a kan kwantiragin na shekara biyu kan fam miliyan biyar.

Park dan kasar Kroea ta Kudu ya bugawa United wasannin Premier 133 tun lokacin da ya dawo kungiyar daga PSV Eindhoven a 2005, inda kuma ya ci kwallaye 19.

United ta dauki kofin Premier hudu da kuma Kofin zakarun Turai daya da dan wasan.

Karin bayani