Terry ya ce Anton Ferdinand na da 'wariyar launin fata'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption John Terry

Dan wasan baya na kulab din Chelsea, John Terry, ya ce Anton Ferdinand na da wariyar launin fata a wani martani da ya mayar bayan da aka zarge shi da yin lalata da tsohuwar budurwar abokin wasansa.

Terry ya bayyana hakan ne a gaban kotu bayan da aka gurfanar da shi game da zarge-zargen.

Ana tuhumar dan wasan, mai shekaru 31, da laifukan da suka shafi kalaman wariyar launin fata sai dai ya sha musanta zargin.

Kotu ta ji cewa Terry ya yi wadannnan kalaman ne a lokacin da kulab dinsa ya buga wasa da QPR, watau kulab din da Anton Ferdinand ke bugawa wasa a watan Oktoba.

An gabatar da wannan kara ce dai a karamar kotun Westminster.

Idan aka samu Mista Terry da laifi dai za a iya cin tararsa pam 2,500.

Karin bayani