Capello na iya zama Kocin Rasha

fabio capello Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Fabio Capello

Tsohon kocin Ingila Fabio Capello da tsohon kocin Tottenham Harry Redknap na daga cikin jerin sunayen wadanda ake saran wani daga cikinsu zai zama sabon kocin kwallon kafa na kasar Rasha.

Hukumar kwallon kafa ta Rasha ta fidda jerin sunayen kociyoyi ciki har da tsohon kocin Barcelona na baya bayan nan Pep Guardiola da kuma na Liverpool Rafael Benitez cikin wadanda Rashan ke son ta dauka aiki domin maye gurbin Dick Advocaat.

Kafin gasar cin Kofin kasashen Turai, Euro 2012, Dick Advoccat ya sanar da cewa zai bar aikin horad da 'yan wasan Rasha domin ya je ya kama aiki da kungiyar PSV Eindhoven.

Haka shi ma kocin Manchester City Roberto Mancini na daga wadanda ake dangantawa da aikin kocin na Rasha kafin zakarun Premiern su sabuntawa kocin nasu dan italiya kwantiraginsa na wasu shekaru biyar.

Karin bayani