Bayar da aron Carroll abu ne mai yiwuwa_Liverpool

Dan wasan tsakiya na kulob din Liverpool, Andy Carroll Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan tsakiya na kulob din Liverpool, Andy Carroll

Kocin kulob din kwallon kafa na Liverpool, Brender Rodgers ya ce ya na duba yiwuwar bada aron dan wasan tsakiya, Andy Caroll.

Dan wasan Ingilan, dan shekaru 23 ya yi ta kokarin ganin ya taka rawar da ake tsammanin ya taka tun lokacin da ya koma kulob din daga kulob din Newcastle.

An sayi dan wasan ne a kan kudi fam miliyan 35 a watan janairun shekarar 2011.

Kudin da kulob din bai taba kashewa wajen sayen wani dan wasa ba.

Kocin kulob din, Rodgers ya ce, " A gaskiya abu ne da ya zama dole in duba".

Sai dai kocin ya ce babu wanda ya yi masa magana a kan sayen dan wasan.

Rahotannin sun ce kulob din Italiya na AC Milan na son aron dan wasan, saboda burge su da ya yi, a gasar cin kofin nahiyar Turai.