Gyan ya koma yi wa Ghana wasa

asamoah gyan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asamoah Gyan

Dan wasan kwallon kafa na Ghana ya Asamoah Gyan ya kawo karshen kauracewa shiga wasannin kasar da ya ke yi.

Gyan dan shekara 26 ya dakata da bugawa Ghana wasa a watan Fabrairu bayan gasar cin Kofin Kasashen Afrika ta 2012.

Dan wasan ya dora alhakin dakatar da bugawa kasarsa wasan a kan damuwar da ya shiga sakamakon bugun-daga-kai-sai-mai-tsaron-gida da ya zubar a wasan kusa da na karshe da hakan ya sa Zambia wadda ta dauki Kofin Kasashen Afrika ta fidda Ghana.

Asamoah Gyan ya shaidawa Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana cewa yanzu a shirye yake ya amsa gayyatar hukumar ta yiwa kasar wasa.

Dan wasan wanda ya kulla yarjejeniyar dun-dun-dun ta yiwa kungiyar Al Ain da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, wasa yace daga yanzu a shirye yake ba tare da bata wani lokaci ba ya bugawa Ghana wasa.

Shugaban Hukumar kwallon Kafa ta Ghana Kwesi Nyantaki yace hukumar ta yaba da matakin da dan wasan ya dauka na sauya shawara, sannan kuma ya yi kira ga 'yan kasar da su rika yin hakuri da 'yan wasa a duk lokacinda aka sami rashin nasara.

Karin bayani