Al Wasl ta kori Maradona

diego mradona Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Diego Maradona

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Al Wasl ta Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, ta kori Diego Maradona daga matsayin kocinta watanni goma sha hudu bayan daukar sa aiki.

Tun a watan Yuni ne ake tantama game da matsayin Maradonan bayan da gaba dayan 'yan hukumar gudanarwar kungiyar su ka ajiye aikinsu saboda kungiyar ta kammala kakar wasanni ba tare da daukar ko da kofi daya ba.

A watan Mayu na 2011 ne Maradona dan shekara 51 ya kama aiki da kulub din kuma har yanzu yana da shekara daya da ta rage masa a kwantiragin.

Kungiyar ta dauko Maradona ne domin ya taimaka mata ta farfado amma ta kare a matsayi na takwas a rukunin kwararru na kasar kuma da bambamcin maki 29 tsakaninta da zakarun lig din kasar Al Ain.

A watan Maris na wannan shekara ce Maradonan ya shiga wajen 'yan kallo domin kare matarsa a lokacin da magoya bayan kungiyar su ke zagin mata da kuma 'yan matan 'yan wasan kungiyar lokacin da kungiyar ta sha kashi a hannun Al Shabab da ci 2-0.

Kungiyar Al Wasl ta Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, ta kori Diego Maradona a matsayin kocinta watanni goma sha hudu bayan daukar sa aiki.

Karin bayani