Villas-Boas na son daga kofi bana

andres villas-boas Hakkin mallakar hoto
Image caption Andres Villas-Boas

Sabon kocin Tottenham Andre Villas-Boas yace yana fatan daukar kofin Premier a bana inda ya ce za su yi kokarin gina kungiyar su kuma dorata a kan hanyar samun nasara, amma kuma ya amince cewa zai sayar da dan wasan kungiyar Luka Modric a farashin da yakamata.

Ya kuma bayyana cewa yana da sha'awar sayo dan wasan tsakiya na Porto Joao Moutinho.

Tsohon kocin na Chelsea, wanda aka sallama daga kungiyar bayan watanni tara kacal ya ce ya taimaka wajen gina harsashin nasarar kungiyar Chelsea a gasar Kofin Zakarun Turai da ta dauka a watan Mayu.

Villas-Boas dan shekara 34 ya kulla kwantiragin shekaru uku da Tottenham, a farkon watan nan domin maye gurbin Harry Redknapp wanda kungiyar ta sallama a watan Yuni.

Duk da nasarar da Villas-Boas ya samu ta kai kungiyar Porto daukar kofin kalubale da na lig na kasar Fotugal da kuma Kofin Europa a kakar wasanni ta 2010 da 2011, kasa da watanni 12 da daukarsa aiki na tsawon kwantiragin shekaru uku kungiyar Chelsea ta kore shi a watan Maris.

Karin bayani