Sojoji 3,500 za su samar da tsaro yayin Olympics

Sojoji 3,500 ne za su samar da tsaro yayin Olympics Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojoji 3,500 ne za su samar da tsaro yayin Olympics

Gwamnatin Birtaniya ta tabbatar da cewa za a tura karin sojoji dubu uku da dari biyar domin sa-ido a kan shingayen hanyoyi a lokacin wasannin Olympics din da za a yi a Landan.

An yanke wannan shawara ce saboda wani kamfanin tsaro mai zaman kansa—G-4S—ya gaza daukar wadatattun ma'aikata a kan lokaci domin wasannin da ake shirin farawa nan da makwanni.

Kamfanin na G4S ne dai ke da alhakin samar da masu gadi dubu goma a duk wuraren da za a yi gasar ta Olympics.

Sai dai kuma a yanzu ta tabbata cewa wannan adadi ba zai samu ba saboda, a cewar kamfanin, ya fuskanci tsaiko wajen tantance masu gadin da yake shirin dauka haya.

Sakatariyar Harkokin Cikin Gida ta Birtaniya, Theresa May, wacce ke da alhakin tabbatar da tsaro lokacin gasar, ta bayyana a gaban Majalisar Dokokin Birtaniya inda ta bayar da karin haske a kan jami'an sojojin da za a yi amfani da su lokacin gasar ta Olympics.

“Shirin ko-ta-kwana na cikin ginshikan tsarinmu na tsaro a Olympics, idan aka samu sauyi a kurarren lokaci; don haka dole ne mu yi wani karin tsari na tsaro don tabbatar da cewa abubuwa sun tafi daidai”, inji Theresa May.

Ta kara da cewa za a baiwa jami'an sojojin, wadanda aka kira a kurarren lokaci don samar da tsaro, kyautar tikitin shiga filayen wasa.

Sai dai kuma 'yan Majalisar Dokokin sun yi mamaki da jin cewa sai yanzu aka gano wannan matsalar.

Daya daga cikinsu ma ya bayyana cewa an jawowa kasar abin kunya.

Mai magana da yawun jam'iyyar adawa ta Labour a kan harkokin cikin gidan Birtaniya, Yvette Cooper, ta bayyana cewa matsalar tsaron ta kara sanya ayar tambaya a kan ko filin tashi da saukar jiragen sama na Heathrow za iya daukar bakin da za su zo domin gasar.

”Na gayawa Sakatariyar Tsaron Cikin Gida [cewa] ya kamata a warware matsalar tsaro da kuma batun shige-da-fice”, in ji Yvette Cooper.

Gwamnati ta nace cewa ba za ta yi sakwa-sakwa ba game da tsaro lokacin Olympics, yayinda Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta ce kasar ba ta fuskantar barazana lokacin gasar.

Amma dai za a iya cewa gwamnati da masu shirya gasar ta Olympics da kuma kamfanin G4S sun yi abin kunya, kwanaki kadan kafin Sarauniya Elizabeth ta jagoranci bikin bude gasar.