Matan Saudi Arabia zasu shiga wasan Olympics

sarah attar Hakkin mallakar hoto IOC
Image caption Sarah Attar

A karon farko Saudi Arabia zata aike da mata cikin tawagarta zuwa wasannin Olympics da za'a yi a London, matan 2 sune na farko da Saudiyyar zata aike zuwa wasannin na Olympics.

Ita dai Wodjan Ali Seraj zata yi gasar wasan a-sakala na Judo ne, yayin da ita kuma Sarah Attar zata yi tseren mita dari takwas.

Saudi Arabia dai tana fuskantar matsin lamba daga babban kwamitin wasannin Olympics da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama akan ta dakatar da tsarinta na aika maza kawai zuwa gasar wasanni.

A karon farko kasashe irinsu Brunei da kuma Qatar da su ma a baya ba su taba aika mata ba, a wannan karon zasu aika.

Karin bayani