BBC navigation

An kebe wuraren da jiragen sama ba zasu bi ba a lokacin Olympics

An sabunta: 14 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 09:24 GMT

Wani sojan saman Burtaniya mai harbi daga boye ke jarraba dabarunsa na yaki a wajen da za a yi wasannin

A yayinda birnin London ke shirye shiryen karbar bakuncin wasannin Olympics nan da makonni biyu masu zuwa, an ware wasu yankuna da ba za a ketara da jirgin sama ba.

Idan wasannin suka kankama dai dakarun saman Birtaniya za su iya amfani da makamai idan jirgi ya shiga yankunan kuma ya ki biyayya ga gargadin cewa ya bar wurin.

Air Vice-Marshal Stuart Atha babban jamiin samar da tsaron sama a wasannin na Olypmpics Ya ce: '' za mu taimaka maka ka bar sararin samaniyar, idan kuwa ka ki amsa umurninmu, kuma ka cigaba da kin yin biyayyar, to ba mu da wani zabi face mu yi amfani da karfi a kanka''.

Wannan dai na daga cikin matakan tsaron birnin na London ke dauka gabanin wasannin na Olympics na shekara ta 2012

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.