Liverpool ta ki amincewa Newcastle akan Carroll

andy carroll Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Carroll

Liverpool ta yi watsi da tayin da Newcastle ta yi mata na karbar Andy Carroll a matsayin aro da nufin maida shi na dundun dun a nan gaba.

Liverpool ta ki amincewa da tayin ne duk kuwa da cewa kocinta Brendan Rodgers ya ce zasu iya bada dan wasan koda a matsayin aro.

Sai dai wasu majiyoyin kusa da dan wasan sun ce shi dai idan so samu ne ya fi son cigaba da zama a Liverppol din domin ya nunawa kocin shi ba kashin yaddawa ba ne.

Idan dai dan wasan bai yi sa'ar tasa tazo daya da kocin ba kuma aka rasa kungiyar da zata biya fam miliyan 35 na daukar sa kudin da Liverpool din ta siyo shi daga Newcastle a watan Janairu na 2011, lalle kulub din zai rasa zabi illa dai ya yi hakuri da farashin da bai kai yadda yake hankoron samu ba.

Karin bayani