Rodriguez na gab da barin Liverpool

maxi rodriguez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Maxi Rodriguez

Dan wasan Liverpool Maxi Rodriguez na duba yuwuwar komawa kungiyarsa ta ainahi dake kasar Argentina Newell's Old Boys.

Dan wasan gaban na Liverpool mai shekaru 30 dake bugawa kasarsa wasa yace ya amince akan manufa ya koma kungiyar wadda ya taso tun yana yaro a cikinta.

Rodriguez ya taso ne daga bangaren matasa na kungiyar ta Nowell's Old Boys wadda ke birnin Rosario na Argentina kafin ya tafi kungiyar Espanyol ta Spain a 2002.

Rodriguez yace shugaban tsohon kulub din nasa William Lorenzo ya kira shi inda ya tambaye shi ko yana da bukatar dawowa kuma ya amsa masa cewa, e. Sai dai dan wasan yace komawar tasa ta dogara ne akan kwantiraginsa da Liverpool.

A kakar wasannin da ta kare Rodriguez ya ciwa Liverpool kwallaye bakwai a wasanni uku, inda a biyu daga ciki ya jefa kwallaye uku-uku.

Karin bayani