AC Milan na neman 'yan wasan tsakiya

'yan wasan ac milan
Image caption 'Yan wasan AC Milan

Kungiyar AC Milan ta Italiya tana neman sabbin 'yan wasan tsakiya sakamakon raunukan da wasu da dama daga cikin manyan 'yan wasanta suka yi,inda Lassana Diarra ke kan gaba cikin wadan da kulub din ke fatan saye.

AC Milan ta na bukatar sayen dan wasan tsakiya a lokacin kakar saida 'yan wasa saboda Sulley Muntari da Rodney Strasser ba zasu sami damar buga wasanni a farkon gasar Serie A dake tafe ba saboda raunukan da suka ji.

A halin yanzu Muntari yana murmurewa daga aikin tiyatar da aka yi masa na raunin da ya ji inda kungiyar ke fatan zai dawo wasa a watan Disamba ,yayin da shi kuma Strasser ake fatan zai warke daga karayar da ya samu a kafa zuwa karshen watan Satumba.

Duk da cewa Lassana Diarra ya na da sauran shekara daya da ta rage masa a kwantiraginsa da Real Madrid, an ruwaito cewa yana shirin barin kungiyar saboda kulub din bai biyashi kudade da yawa ba a kakar wasannin da ta wuce.

Kungiyar ta Serie A tana kuma neman wani dan wasan na gaba da zai maye gurbin Zlatan Ibrahimovic wanda ke shirin komawa Paris Saint-Germain, kuma ana ganin ta na neman Carlos Tevez da Edin Dzeko na Manchester City.

Karin bayani