Liverpool ta ki ba Necastle aron Carroll

Andy Carroll mai riga lamba tara Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Andy Carroll mai riga lamba tara

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ce ba za ta baiwa kulob din Newcastle aron dan wasan tsakiyarta Andy Carroll ba.

Kulob din Newcastle ta yi tayin karbar aron dan wasan a kan albashi fam dubu 80 a kowane mako.

Kuma Newcastle na son Liverpool ta sayar mata da Carroll a kan wani farashi a kakar wasanni na shekara mai zuwa.

Sai dai tayin na Newcastle bai kai abin da Liverpool ke tsammani ba wajen ba da aron dan wasan.

Liverpool ta yi watsi da tayin a ranar lahadi, saboda ta fi son ta sayar da dan wasan a maimakon ba da shi aro.