Dole ne a dauki mataki akan John Terry- Amaechi

John Terry a harabar kotu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu masu rajin yaki da launin fata na bukatar a dauki mataki kan Terry

Wani mai rajin yaki da nuna wariyar launin fata John Amaechi ya bayyana cewa dole ne hukumar kwallon kafa ta FA ta dauki mataki mataki akan John Terry.

Amaechi na daya daga cikin 'yan wasan kwallon kwando a Burtaniya da su ka shahara bayan ya share shekaru a NBA tare da Cleveland Cavaliers da Orlando Magic da kuma Utah Jazz.

Kuma a yanzu ya yi ritaya kuma yana aiki a matsayin dan agaji

Wata kotu dai ta wanke dan wasan na Chelsea John Terry saboda cin mutuncin Anton Ferdinard na QPR.

Amma hukumar kwallon kafa ta FA ka iya sanya wa John Terry takunkumi saboda wata hujja ta daban.

John Amaechi ya kara da cewa hatsarin shine bakaken fata a wasan kwallon kafa zasu soma yiwa hukumar kwallon kafar FA wani irin kallo.