Ledley king ya daina buga wasan kwallon kafa

ledley king Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Ledley King

Dan wasan Tottenham, Ledley King, ya rataye takalmansa na kwallo ya kuma yi sallama da buga tamola saboda raunin da ya ke fama da shi.

Sai dai har yanzu tana jika domin yace zama daram a Tottenham din saboda karar da kungiyar ta yi masa ta nada shi jakadanta.

Tsohon dan wasan na Ingla mai shekaru 31, raunin da ya saka shi a gaba tsawon shekaru da ya hana shi samun sukunin motsa jiki akai-akai shi ya tilasta masa barin wasan.

A karshen kakar wasanni ta 2012-2013 ne Tottenham zata yi wasan karrama dan wasan wanda tun yana matashi ya ke tare da kungiyar din.

Karin bayani