Mohammed Bin Hammam ya yi nasara a kotu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban hukumar kwallon kafa na duniya Sep Blatter

Kotun sauraron laifuka kan wasanni ta soke dokar da ta haramtawa tsohon dan takarar shugabancin Hukumar kwallon kafa ta Duniya watau FIFA Mohammed Bin Hammam aiki har tsawon rayuwarsa game da tuhumar da ake masa ta bada cin hanci.

An zargi Mohammed Bin Hammam da yunkurin sayen kuri'u gabanin zaben shugabancin Hukumar Kwallon kafa ta duniya da aka yi a bara.

Daga bisani hukumar ta FIFA ta haramtawa Bin Hammam gudanar da wani aiki da ya shafi kwallon kafa a cikin kasarsa da kuma kasashen duniya.

Sai dai kotun ta ce ba bu wata kwakkwarar hujja dake nuni da cewa ya aikata laifi, ko da yake kotun ta ce hukuncin ba wai yana nufin cewa ta wanke Mr Hammam daga tuhumar da ake masa ba ne.

Mohammed Bin Hammam me shekaru sittin da biyu da tsohon mataimakin shugaban hukumar ta FIFA Jack Warner ,an dakatar dasu daga aiki ne sakamakon wani rahoto da ya nuna cewa an baiwa jamian hukumar kwallon kafa ta kasashen Carribbeans su hudu cin hanci ko kuma lamarin ya faru ne a gabansu a taron da aka yi a watan Mayu na bara.

Karin bayani