Tilas a cimma matsaya akan Modric - Inji Villas-Boas

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Luka Modric

Kocin Tottenham Andre Villas-Boas ya gargadi kulob-kulob din dake zawarcin siyan dan wasan tsakiya Luka Modric kan cewa sai sun saye shi akan fam miliyan 35.

Ya zuwa yanzu dai kungiyoyi uku ne ke zawarcin wannan dan wasa,inji Villas-Boas.

Kulob-kulob din dake zawarcin dan wasa sun hada da Real Madrid,da Manchester United da kuma Paris St-Germain.

Villas-Boas ya ce,"yana da kyau a fahimci yadda wannan dan wasa ke ji a ransa game da barin Tottenham. Muna magana dashi,mun kuma fahimci manufarsa, shima ya fahimci manufar kulob din."

Dan wasa Modric wanda ya fara taka leda a kulob din Tottenham daga Dinamo Zagreb a shekarar 2008,da farko ya nuna sha'awarsa ta barin White Hart Lane a bara,amma sai Tottenham taki amincewa da wannan bukata tasa.

Karin bayani