Kungiyoyi 3 sun yi tayin sayen Van Persie

Van Persie Hakkin mallakar hoto
Image caption Robin Van Persie Kyaftin din kungiyar Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta karbi tayin sayen Kyaftin din ta Robin Van persie daga kungiyoyin Manchester City, da Manchester United da, Kuma Juventus.

Dan wasan gaban mai shekaru 28 ba zai shiga cikin tawagar 'yan wasan Arsenal din da zasu je nahiyar Asia ba ranar Assabar domin buga wasu wasanni uku na share fagen shiga sabon zangon wasanni.

Bayanai sun nuna cewar duka kungiyoyin uku sun yi tayin sayen dan wasan ne a kan kimanin Fam miliyan 15 amma Arsenal suna sha'awar sayarda shi ne a kan Fam miliyan 25 zuwa 30.

Dan wasan mai kai hari, wanda ya je kungiyar Arsenal daga Feyenoord akan kudi fam miliyan 2.75 shekaru takwas da suka gabata, ya ciwa kungiyar da kuma kasar sa watau Netherlands kwallaye 41 a cikin wasanni 53 a kakar wasanni ta bana.

Karin bayani