Ramsey na fatan Van Persie ya tsaya

robin van persie Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Robin van Persie

Dan wasan tsakiya na Arsenal Aaron Ramsey na son ganin Robin van persie ya cigaba da zama a kulub din.

Ramsey wanda ya ke cikin tawagar 'yan kwallon kafar Burtaniya ta wasannin Olympics yace van Persie yayi rawar gani sosai a kakar wasan da ta wuce kuma babban dan wasane a wurinsu saboda haka suke fatan ya tsaya.

Ramse yace basu san abin da ke wakana tsakanin dan wasan da shugabannin kungiyar ta Arsenal ba a halin yanzu, amma dai babban fatansu shi ne van Persie ya tsaya a kulub din.

Kungiyar Arsenal ta yi watsi da bukatar dan wasan da kungiyoyin Manchester United da Manchester City da kuma Juventus su ka gabatar mata akan van Persien.

Sauran shekara daya ta ragewa Van Persie dan shekara 28 , a kungiyar ta Arsenal wadda yace ba zai sabunta kwantiraginsa da ita ba.

Van Persie ya ciwa Arsenal kwallaye 37 a kakar wasannin da ta wuce, 30 daga ciki a wasannin premier, ya zama zakaran dan wasan Kungiyar kwararrun 'yan wasa ta Ingila ,PFA da kungiyar marubuta wasanni kuma ya taimakawa kungiyar ta Arsenal ta farfado a gasar premier da ta gabata har ta zama ta uku.

Karin bayani