Luka Modric zai biya tara

Luka Modric, dan wasan Tottenham Hakkin mallakar hoto
Image caption Luka Modric, dan wasan Tottenham

Za a ci tarar dan wasan kungiyar kwallon kafa na Tottenham, Luka Modric, saboda rashin halartar horarwa.

Haka kuma dan wasan bai halarci wasannin share fagen kakar wasannin kulob din ba.

Manajan Tottenham, Andre Villas-Boas ya ce "Ina ganin cewa Modric bai yi adalci ba saboda abin da ya yi ya sa shugaban kungiyar Daniel Levy ya yi fushi."

Andre ya jaddada cewa sakamakon wannan kuskure da Modric ya yi zai rasa albashin mako biyu.

Sai dai kuma, Villas-Boas ya amince cewa Kulob din na Spurs zai yi babbar asara idan Modric ya tafi saboda kwarewarsa.