Koscielny ya sa hanu akan sabon kwantaragi a Arsenal

Arsenal Hakkin mallakar hoto
Image caption Laurent Koscielny dan wasan Arsenal

Kulob din Arsenal ya sanar cewa 'dan wasan baya Laurent Koscielny ya amince da sabon kwantaragi na tsawon wa'adi a kulob din.

Dan wasan kwallon kafa na kasar Faransa me shekaru ashirin da shida, ya taka rawar gani tun lokacin da ya fara taka leda a Arsenal shekaru biyu da suka wuce daga kulob din Lorient.

"Laurent ya nuna kwazo sosai tun lokacin da ya fara taka leda a Arsenal."Inji kocin Arsenal, Arsene Wenger.

Shawarar da 'dan wasan ya yanke, ta zo ne a dai -dai lokacin da dan wasan gaba Robin Van Persie ya ce ba zai sabunta kwantaraginsa da Arsenal ba.

Wa'adin kwantaragin Van Persie a Arsenal zai zo karshe a kakar wasanni mai zuwa kuma 'dan wasan dan kasar Netherlands na neman wani sabon kulob da zai fuskanci kalubale bayan shekaru takwas da ya shafe a Arsenal din.

"Ina farinciki game da yarjejeniyar da muka cimma da Arsenal, saboda na ji dadin zama na a kulob din."Inji Koscielny.

Babu wani dan wasan da ya bugawa Arsenal kwallo fiye da shekaru biyu da suka wuce kamar Koscielny, saboda wasanni tamanin da biyar ya bugawa Arsenal tun lokacin da ya fara taka leda a kulob din a shekerar 2010.