Kompany ya sanya hannu a sabon kwantiragi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vincent Kompany

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya sanya hannu a sabon kwantiragi da kulob din na tsawon shekaru shida.

Matashin mai shekaru 26, dan asalin kasar Belgium ya shiga kungiyar Manchester City daga Hamburg ne a watan Agustan 2008.

A karshen kakar wasan da ta wuce, Kompany ya jagoranci kulob din inda suka dauki kofin gasar Premier a karon farko tun shekarar 1968.

Kompany ya ce: “A ganina idan dan wasa ya samu karbuwa a wani wuri, ba shi da amfani ya bar wurin; kuma karbuwar da na samu daga magoya bayan kulob din ce ta kara min karfin gwiwar sanya hannu a sabon kwantiragin nawa.”

Ya kara da cewa, :''Na dade a wannan kulob din kuma na ga fari da bakinsa; saboda haka nima ina jin na bayar da tawa gudunmawar kuma na ji dadi da kungiyar ta yi la’akari da gudunmawata. Sanin cewa zan kara wasu shekaru shida a kulob din nan na faranta min rai.”

Karin bayani