An nemi afuwar Koriya Ta Arewa game da Olympics

Image caption Jami'an Korea Ta Arewa a gasar Olympics

Masu shirya gasar Olympic sun nemi afuwa daga kulob din kwallon kafa na mata na Koriya Ta Arewa saboda kuskuren da aka yi na nuna 'yan wasan a talabijin kusa da tutar Koriya Ta Kudu.

Kuskuren dai ya sanya an jinkirta wasan da kulob din matan zai buga a Hampden Park da ke Glasgow a ranar farko da aka fara wasan.

'Yan kulob din maza na Koriya ta Areawa za su fara gasar ne a lokacin da za a buga wasanni takwas ranar Alhamis, ciki har da wanda za a buga tsakanin Burtaniya da Senegal a filin wasa na Old Trafford.

Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron, ya shaidawa BBC cewa, gasar na da matukar muhimmanci.

Ya ce: ''Babban abin da ke da muhimmanci game da gasar shi ne yadda za ta kasance wani abin koyi ga 'yan baya. Mutane za su shigo kasarmu a cikin makonnin da ke tafe, don haka wasan wani abin alfahari ne''.

Karin bayani