Burtaniya da Senegal sun yi kunnen doki

Gasar wasannin olympics Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Moussa Konate dan wasan Senegal

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na Senegal ta yi kunnen doki daya da daya da ta Burtaniya a karawar da suka yi a filin wasa na Old Trafford.

'Yan wasan kwallon kafar na Burtaniya sun shafe shekaru 52 ba su buga a gasar Olympics ba.

A rabin lokaci na farko na wasan dan wasan Burtaniya Craig Bellamy ya fara sa kwallo a cikin ragar Senegal.

Sai dai 'yan wasan Lions of Teranga na Senegal, wadanda ke halartar gasar Olympics din a karo na farko, sun maida martani da kwallon da Moussa Konate ya zura a cikin raga Burtaniya ana saura mintuna goma a kammala wasan.

A cewar 'yan wasan na Burtaniya ba su ji dadin yadda 'yan Senegal suka yi wasa ba saboda sun yi amfani da karfin tuwo.

Wannan dai ya sa an kasance kunnen doki a rukunin A: yayin da Burtaniya ke shirin kammala sauren wasan ta da tawagar Hadadiyar Daular Larabawa watau UAE da kuma ta kasar Uruguay ranar Laraba mai zuwa.