Adam Matsoraci ne, in ji Bale

gareth bale Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gareth Bale

Dan wasan kungiyar kwallon kafa na Tottenham Gareth Bale ya kira Charlie Adam matsoraci bayan dan wasan na Liverpool ya ji masa rauni a karo na biyu.

A shekara ta 2011 Bale ya bar wasa tsawan watanni uku saboda wani rauni da Adam ya ji masa a lokacin yana Blackpool.

Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce Adam ya sake jiwa Bale rauni a lokacin wasan sada zumunta da Liverpool da Tottenham a Baltimore ta Amurka wanda a kan hakan Bale yace Charlie Adam matsoraci ne.

Bale yace "a duk lokacin da dan wasa yayi maka keta kana tsammanin ya baka hakuri, to bai bani hakuri ba kuma ko da ya bani hakurin ma bazan hakura ba".

Shi ma dan wasan baya na Tottenham Kyle Walker ya bi sahun sukan Adam in da yace "Gareth dan wasa ne mai kyau da yake bukatar kariya "

Yace "bai kamata yan wasa su tsane shi ba, kamata yayi su so yin wasa tare da shi domin za su koyi wani abu daga gare shi maimakun su runka yi masa keta".

Karin bayani