Rabecca za ta kwato kambunta

Dakin wasan ninkaya na Olympics Hakkin mallakar hoto Daniel Ramalho
Image caption Dakin wasan ninkaya na Olympics

'Yar wasan ninkaya ta Birtaniya Rabecca Adlington ta ce za ta zage damtse dan ganin ta rike lambar yabonta a gasar ninkaya da za a yi a ranar alhamis.

Tauraruwar wasan olympics ta shekarar 2008, tana ji tana gani dan wasa France's Camille Muffat ya kwace mata kambunta, a yayin da dan wasan Amurka Allison Schmitt ya dauki azurfa.

Game da wasan ninkaya na mita 800 da za a yi a ranar Alhamis da kuma zagayen karshe a ranar Juma'a,'yar wasan ta ce

"Na san babban aiki ne ninkaya har ta mita 800, kamar yadda ninkaya na mita 400 yake''.

Adlington ta kara da cewa ''amma duk da hakan zan yi iyakar kokari na kamar yadda na yi a ranar lahadi.

Kuma ina sa ran 'yan kallo za su kara mini kwarin gwiwa kamar yadda su ka yi a baya, wannan zai taimaka mini wajen samun nasara''