Jack Wilshere ba zai buga wa Arsenal wasa ba

jack wilshere Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jack Wilshere

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce Jack Wilshere ba zai buga wa kungiyar wasa ba kafin watan Oktoba.

Dan wasan tsakiyar mai shekara 20 da haihuwa ya shafe tsawon kakar wasanni daga 2011-2012 yana jiyya saboda raunin da ya yi a idon sawu da kuma tiyatar da aka yi masa a watan Mayu.

"Muna sa ran cewa a cikin watan Oktoba Wilshere zai dawo wasa inda zai buga wasan karshe na zagayen kasashen Asia a Hong Kong ", in ji Wenger .

Wilshere na fatan zai dawo horo kadan kadan a cikin watan Agusta.

Karin bayani