Sayar da hannun jarin United ya jawo ce-ce-ku-ce

'yan wasan Manchester united Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Manchester United

Maganar sayar da hannun jarin Manchester United ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya baya wadanda suka mallaki jari a kungiyar da Iyalan Glazers Amurkawa masu jari a kungiyar.

Takaddamar ta taso ne saboda masu jari a Kungiyar ta Manchester United, Iyalan Glazers dake Amurka, na son samarda dala miliyan 330 ta hanyar sayar da hannun jarin kungiyar a Kasuwar Hannun Jari ta New York, wato Wall Street, ba tare da yin amfani da kudaden wajen biyan bashin da ake bin kungiyar na dala miliyan 680 ba.

Masu kungiyar dai sun tsara cewa kaso mafi yawa na kudin da za a samu daga sayar da hannu jarin zai je wurinsu ne maimakon rage bashin dake kan Kulob din.

Haka kuma tsarin sayarda hannun jarin kulob din a kasuwar Hannun jarin ta Amurka ya nuna cewa Iyalan Glazers din wadanda jarinsu a kungiyar bai kai darajar na magoya bayan kungiyar ba suna da ikon kuri'a ribi goma akan ikon da magoya bayan suke da shi.

Shugaban Asusun magoya bayan kungiyar ta Manchester United, Duncan Drasdo yace dole ne magoya bayan su damu akan tsarin ganin cewa daman tun a baya Iyalan Glazers din sun jawo wa kungiyar kusan bashin dala miliyan 550.

Karin bayani