Kulob din Dynamo ya dauki aron Taye Taiwo

Taye Taiwo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taye Taiwo

Kulob din kwallon kafa na kasar Ukrain Dynamo Kiev ya dauki aron dan wasan Najeriyar nan Taye Taiwo a tsawon kakar wasanni.

A bara ne Taye ya koma Milan daga Marseille, amma ba a sa shi buga wasanni sosai, abin da ya sa aka bada aron shi ga kungiyar QPR.

Taye ya shaidawa BBC cewa " Komawata Ukrain wata dama ce da zan dinga bugawa kulob din wasa a kodayaushe."

Ya kara da cewa " Na san Milan kulob ne mai kyau, amma ni ba dan wasa ba ne dake farin ciki da zaman benci ba tare da buga wasa ba, sai dai kawai in yita karbar albashi. "

Kulob din na Dynamo Kiev na da zabin ya sayi Taye a karshen kakar wasanni a kan kudi euro miliyan biyu.