Arbeola ya sabunta kwantiraginsa da Madrid

alvaro albeloa Hakkin mallakar hoto g
Image caption Alvaro Albeloa

Dan wasan Spain dake bugawa Real Madrid wasa Alvaro Arbeola ya sake kulla yarjejeniyar kwantiragin karin shekaru biyu a kungiyar.

Da wannan kwantiragin Arbeola mai shekara 29 zai cigaba da zama a kulob din har zuwa shekara ta 2016.

Dan wasan dai ya taso ne daga kungiyar matasan 'yan wasan Real Madrid amma ya bar kungiyar zuwa Deportivo La Coruna a 2006 sabo da ba a sa shi a cikin jerin 'yan wasan Real din na farko dake yin wasa akai-akai ba.

Sai dai dan wasan ya sake dawo wa Real Madrid din a 2009 bayan shekaru biyu da rabi a kungiyar Liverpool kuma tuni ya zama daya daga cikin 'yan wasan da Jose Mourinho ya fi ji da su a kulob din.

Dan wasan yace kara tsawon kwantiragin nasa da kungiyar ta yi girmamawa ce a gare shi kuma abin farin ciki ne, ganin yadda kulob din ya yarda da shi.

Dan wasan bayan, sau 123 yana bugawa Real Madrid wasa kuma sau uku yana ci mata kwallo.

Karin bayani