BBC navigation

Oscar Pistorius ya kafa tarihi a Gasar Olympics

An sabunta: 4 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:22 GMT
Oscar Pisterius

Dan tseren Afirka ta Kudu Oscar Pisterius

Dan wasan tseren nan na Afirka ta Kudu, Oscar Pistorius, wanda ’yan kallo suka fi sani da Blade Runner, ya zama mutum na farko mara kafafu da ya fafata a Gasar Olympics.

Pistorius, wanda ke gudu da kafaunsa na karfe, ya zo na biyu a rukunin da yake na tseren mita dari hudu na maza a London, al'amarin da ya ba shi damar shiga zagaye na gaba.

Bayan nasarar tasa, Oscar Pistorius ya bayyana cewa ya ma rasa me zai yi: “In yi kuka ne ko in yi murna; amma dai na yi tunanin cewa akwai aiki a gaba na saboda haka na zage dantsa na kai ga gaci”.

Lambobin zinare ashirin da biyar ake sa ran lashewa a yinin yau, wanda shi ne yinin da ya fi ko wanne yawan wasanni ya zuwa yanzu tun farkon gasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.