Olympics: 'Yar Afrika ta kara lashe lambar Zinari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'yar wasar ninkayar Togo Adzo Kpossi

A gasar wasannin Olympics da ake yi birnin London an fara lashe lambobin yabo a fagen tsere da sauran wasu wasannin na motsa jiki a babban dandalin wasannin.

A tseren mita dubu goma na Mata, 'yar kasar Ethiopian nan zakara a tseren na Olympics Tirunesh Dibaba ta cinye lambar zinariya inda ta cigaba da rike matsayin ta.

Wani zakaran kuma na gasar jefa nauyi Tomaz Majewski dan kasar Poland shi ma ya cinye lambar zinariya yayinda ya cigaba da rike matsayinsa.

A gasar ninkaya kuwa Michael Phelps ne dan kasar Amurka ya cinye tseren na mita dari ya kuma cinye lambar zinariya karo na ukku a gasar wasannin na London, kuma karo na goma sha-bakwai a tsawon sana'ar sa.

Karin bayani